Shugaban Ƙasar Zimbabwe mai shekaru 80, Emmerson Mnangagwa, ya nuna ra’ayinsa na sake maimara wasu shekaru a kujerar shugabancin ƙasar.
Shugaba wanda ya kasance shugaban Ƙasar Zimbabwe na biyu tun bayan dogon mulkin shugaba Robert Mugabe da ya shafe shekaru kusan 40 a mulki.
Emmerson Mnangagwa, shi ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa Mugabe, ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar bayan juyin mulkin, ya kuma yi alƙawarin bunƙasa tattalin arziki ƙasar, da bayar da ‘yancin faɗin albarkacin baki, da sassauta takurawar da ake yi wa ‘yan adawar da ke magantuwa kan wa’adin mulkin Mugabe, da kuma taɓarɓarewar dangantaka da ƙasashen yammacin duniya.
Ko da yake abin ba haka yake ba a shekaru biyar da suka gabata, lokacin da Zimbabwe ta shirya gudanar da zaɓenta na farko tun bayan juyin mulkin da ya kawo ƙarshen mulkin da ake masa kallon na danniya na shekaru 37 da tsohon Shugaba Robert Mugabe ya iba yana yi.
Domin an yaba wa Mnangagwa ɗa matsayin shugaba na gaskiya jim kaɗan bayan hawansa mulki, sai dai ya samu ‘yar ƙaramar nasara a zaɓen 2018 a kan Chamisa, wanda har yanzu ake ganin shi ne mai ƙalubalantar sa a karo na biyu.
A shekaran jiya Laraba ne al’ummar Zimbabwe ke kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisa da ke zuwa a cikin wani mawuyacin hali na taɓarɓarewar tattalin arziki. An yi hasashen zai zama mai cike da ƙalubale, yayin da ake ganin jam’iyyar adawa za ta kwashe ƙuri’un matasa, sai dai har yanzu jam’iyyar ZANU-PF ce ke kan gaba a zaɓen.
Akwai ‘yan takara 11 da ke neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen da wakilan ƙungiyoyi daban daban na duniya ke sanya ido a kai.
Shugaban jam’iyyar ZANU-PF mai mulki Emmerson Mnangagwa mai shekaru 80 da haihuwa, yana adawa da Nelson Chamisa, mai shekaru 45 lauya kuma fasto da ke jagorantar jam’iyyar adawa ta CCC.
Zaɓen na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da taɓarɓarewar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki.
Ana zargin gwamnati da yi wa mulkin dimokuraɗiyya karan-tsaye bayan zartar da wani ƙudirin doka da ake kira Patriotic Bill, wanda ‘yan adawa ke cewa ya sava wa ƙa’ida.