Shugaban Ƙasar Nijar ya ziyarci wurin gina madatsar ruwa ta Kandadji

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Nijer Mohamed Bazoum da ministocin makamashi, da tsaron ƙasa, da harkokin cikin gida da sauran wasu ministocin ƙasar, sun ziyarci wurin gina madatsar ruwa ta Kandadji tare da jakadan Sin dake ƙasar, Jiang Feng.

A yayin ziyarar ta safiyar jiya, shugaba Bazoum ya bayyana cewa, ƙasar Nijer ta gamsu da aikin gina madatsar ruwan, yana mai cewa kamfanin Sin mai aikin ginin ya shahara a duniya.

A cewarsa, kamfanin na Sin ya tura ƙwararru zuwa wurin don sa kaimi da kyautata tsarin gudanar da aikin. Za a kammala gina madatsar ruwan ne a karshen shekarar 2025, inda Niger za ta ga cikar burinta.

A nasa ɓangare, jakada Jiang Feng ya bayyana cewa, Sin da Nijer sun ƙulla zumunci mai zurfi, kana Sin tana ba aikin ginin madatsar ruwan Kandadji muhimmanci, kuma za a ci gaba da sa ƙaimi ga aikin don tabbatar da gama shi akan lokaci, domin ba da gudummawa ga sha’anin samar da makamashi na ƙasar Nijer.

Mai fassara: Zainab