Shugaban Ƙasar Sin ya yi shawarwari da manyan Sshugabannin Ƙasar Saudiyya da kuma gana da shugabannin wasu ƙasashen Larabawa bi da bi

Daga CMG HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da sarkin masarautar Saudiyya, Salman bin Abdul Aziz Al Saud a fadarsa dake birnin Riyadh a ran 8 ga wata da yamma, agogon wuri.

Xi ya ce, kasarsa ta mayar da Saudiyya a matsayin wata muhimmiyar kasa dake taka rawar gani a harkokin duniya, inda take fatan kara mu’amalar manyan tsare-tsare tare da Saudiyya, da zurfafa hadin-gwiwa a bangarori daban-daban, a wani kokari na kiyaye moriyarsu, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

A nasa bangaren, sarki Salman ya yi marhabin lale da zuwan shugaba Xi, inda a cewarsa, yana matukar maida hankali kan raya dangantaka tare da kasar Sin, da kuma bayyana fatansa na samar da ci gaban huldodin kasashen biyu, bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkanin fannoni.

Shugabannin biyu sun kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar kulla dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkanin fannoni, tsakanin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin da kasar Saudiyya, inda suka amince cewa, za su gana a kasashensu a kowace shekara.

A dai wannan rana, shugaba Xi ya yi shawarwari tare da yariman masarautar Saudiyya, kana firaministan kasar Muhammad bin Salman bin Abdel Aziz Al Saud, inda suka yarda cewa, za su daga matsayin shugabancin kwamitin hadin-gwiwar manyan jami’an kasashen biyu, zuwa matsayin firaminista.

Shugabannin biyu sun kuma halarci bikin mika wa juna takardun yarjeniyoyin hadin-gwiwar kasashensu, a fannonin da suka shafi raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da aikin shari’a, da ilimi, da makamashin hydrogen, da zuba jari, da gidajen kwana da sauransu.

Bayan shawarwarin, shugaba Xi ya halarci bikin maraba da yariman Muhammad ya shirya masa, a madadin sarkin Salman bin Abdul Aziz Al Saud.

Sannan a wannan rana da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kuma gana da takwaransa na kasar Masar, Abdel Fattah al Sisi a Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya.

Yayin ganawar, Xi ya ce, bisa halin da ake ciki yanzu a duk duniya, da ma shiyyoyi daban-daban na fuskantar manyan sauye-sauye, yana da muhimmanci a raya huldodin Sin da Masar bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoi. Ya ce ya dace kasashen biyu su yi kokari tare, don neman cimma burin gina al’ummominsu masu kyakkyawar makoma ta bai daya, ta yadda za’a kara samar da sabon ci gaba, ga dangantakarsu bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni.

A nasa bangaren, shugaba Sisi ya ce, ya zo kasar Sin don halartar bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da aka yi a watan Fabrairun bana a Beijing, inda ya yi shawarwari masu gamsarwa tare da shugaba Xi. Ya ce, ya ziyarci kasar Sin a wancan lokacin ne don goyon bayan kasar, da karfafa dangantaka tare da kasar.

Sisi yana da yakinin cewa, a sabon wa’adin aikin shugaba Xi, dangantakar kasashen biyu za ta samu karin ci gaba, kana, kwalliya za ta biya kudin sabulu, wajen karfafa hadin-gwiwarsu a bangaren shawarar “ziri daya da hanya daya”.

Bugu da kari, da safiyar yau 9 ga wata ne, bi da bi shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwarorinsa na kasar Tunisiya Kais Saied da na kasar Mauritaniya Mohamed Ould Ghazouani da na kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh da na kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud da na Comoros Azali Assoumani da firaministan kasar Iraki Mohammed Shia al-Sudani da sarki Tamim Bin Hamad Al Thani na masarautar Qatar a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya.

Mai fassara: Murtala Zhang, Ibrahim Yaya