Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya bayar da bayani kan halin da Gavi da Ousmane Dembele ke ciki a ƙungiyar. Ya ce, ɗan wasan da kwantiraginsa ya ƙare zai ci gaba da zama yayin da a ƙarshen zai karɓi tayin da ya ke da shi idan yana son cigaba da zama.
Da ya ke magana game da Gavi, Laporta ya ce, “Gavi zai cigaba da zama ɗari bisa ɗari tare da Barca, muna da yarjejeniya da shi.”
Gavi, mai shekaru 17, ana ɗaukarsa a halin yanzu ɗaya daga cikin samari masu kwarin gwiwa a fagen ƙwallon ƙafa a duniya. Ɗan wasan ya samu hazaƙa a kakar wasan da ta wuce, inda ya buga wa Barcelona manyan wasanni 46 a dukkan gasa sannan kuma ya ci ƙwallaye biyu da taimakawa shida.
Ɗan wasan na Spain ya kuma samu buga wasanni 10 na ƙasa da ƙasa. Yanzu da alama yana shirin cigaba da zama a Camp Nou.
A halin yanzu, makomar Dembele tare da Barcelona har yanzu tana kan tudu. Kwantiraginsa da kulob ɗin ya ƙare a bazarar da ta gabata kuma har yanzu bai amince da sabon tayin da suka yi ba. Da ya ke magana game da halin da ya ke ciki.
Laporta ya ce ta hanyar Fabrizio Romano kuwa, “Idan yana so ya zauna, dole ne ya amince da buƙatarmu ta ƙarshe – in ba haka ba zai tafi. Babu ranar ƙarshe ta datse tayin mu. Muna son Ousmane ya ci gaba amma yanzu ya dogara da shi. Bai yarda da shawarar mu ba yanzu amma a buɗe ta ke.”
Dembele, mai shekaru 25, ya yi fama tun bayan komawarsa ƙungiyar akan Yuro miliyan 105 daga Borussia Dortmund a shekarar 2017. Matsalolin raunin da ya ji sun ƙayyade shi zuwa wasanni 150 a Blaugrana a dukkan gasa, inda ya ci ƙwallaye 32 kuma ya taimaka 34.
An danganta ɗan wasan na Faransa da tafiya a cikin kasuwar musayar ’yan wasa ta Janair. Duk da haka, tashinsa a ƙarƙashin Xavi Hernandez ya sa ya zauna a Camp Nou. Ya taimaka 13 sannan ya zura ƙwallaye biyu a wasanni 21 da ya buga a gasar La Liga a bara.