
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon wakilin Gwamnatin Amurka kuma babban jami’in kamfanin Binance, Trigram Gambaryan, ya bayyana zargi mai ban mamaki akan Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, bayan fitowarsa daga komar hukuma.
Tun a watan Junairun 2024 ne Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin a tsare Mista Gambaryan kan zargin sa da hannu a badaƙalar kuɗaɗe.
A wani dogon saƙo da ya wallafa a kafar sadarwa, Gambaryan ya ce, ya fuskanci matsalolin shiga haramtattun ayyuka ciki har da wanda ke da alaƙa da Malam Nuhu Ribaɗu.
A cewarsa, Ribaɗu ya wuce gona da iri da tozarta Nijeriya a idon tsohon Mai Ba Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro na Amurka, Jake Sullivan, wanda hakan ya haifar da rashin nasara a harkar diflomasiyya.
Ya ce, lamarin ya sabbaba taƙaice bada bisa ga tawagar Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka yi a Amurka da kuma ƙin ganawa da Shugaba Tinubu da tsohon Shugaban Ƙasar, Joe Biden ya yi, wanda har sai da aka warware matsalar.
A lokacin da ya ke magana game da zamansa a hannun hukuma, Gambaryan ya ce, wasu daga cikin jami’an gwamnati sun bayyana son kai, inda ya ce Ribaɗu ya nuna yana da buƙatar biliyoyin kuɗi don cimma manufofinsa na ɗaukar nauyin takarar siyasa a gaba.
Ya ƙara da cewa, a lokacin da aka tada zargin rashawa akan batun, Ribaɗu ya shiga halin tsaka-mai-wuya ganin cewa akwai yiwuwar a jingina masa karɓar cin-hanci, wanda haka ka iya sanya a tsige shi daga muƙaminsa.
Har’ilayau, Gambaryan ya ce da farko Ribaɗu ya yi tunanin samun nasara cikin sauƙi, wanda hakan bai samu ba kasancewar al’amarin ya kai mataki na ƙasa-da-ƙasa da kuma nuna rashin ƙwarewarsa a idon duniya.