Shugaban Haɗaɗɗiyar Daularar Larabawa, Kalifa bin Zayed ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kuma ɗaya daga cikin attajiran sarakunan duniya, Sheikh Khalifa bin Zayed al-Nahyan ya rasu.

Sheikh Khalifa wanda ya bar duniya yana da shekara 73, ya soma mulkinsa ne tun a 2004, duk da dai galibi mataimakansa ke gudanar da harkokin mulki a madadinsa tun bayan da ya kamu da lalurar shanyewar ɓarin jiki a 2014.

A halin da ake ciki, ɗan uwan marigayin Mohamed bin Zayed al-Nahyan, shi ne ke kula da sha’anin mulkin daular.

Kamfanin dillancin labarai na WAM da ke daular, shi ne ya ba da sanarwar rasuwar basaraken.

A matsayinsa na shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a halin rayuwarsa, marigayi Sheikh Khalifa shi ke mulkin Abu Dhabi mai arzikin mai kuma babbar cibiyar masarautu bakwai haɗe da UAE.

An yi amannar cewar ƙarfin arzikin marigayin ya kai Dala biliyan $150bn wanda ya yi daidai da biliyan £123.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *