Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Fira Ministan Spain Pedro Sanchez ya caccaki shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasar Sifaniya, Luis Rubiales, kan yadda ya sumbaci ‘yar wasan da ta lashe gasar kofin duniya ta mata Jenni Hermoso.
A cewar Fira Ministan, bayar da haƙuri kan lamarin kawai ba zai isa ba idan aka yi la’akari da girman abin da ya faru.
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar Sifaniya, Luis Rubiales ya nemi afuwa sakamakon sumbatar ’yar wasan tawagar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasar, Jenni Hermoso da ya yi a leɓe, bayan da suka lashe kofin duniya ta mata da aka kamala a ƙarshen makon da ya gabata.
Rubiales ya sumbaci ’yar wasan gaba ta tawagar ƙwallon ƙafar matan Spain a lebenta a yayin da ake miqa musu kyautukan da suka lashe bayan wasan karshe da suka fafata da Ingila a ranar Lahadi.
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Rubiales ya ce bai kyauta ba, kuma abin da ya yi bai dace ba. Ya ƙara da cewa ba ya yi ne da mugun nufi ba, tsabagen farin ciki ne kawai.
Rubiales ya sha suka daga wasu daga ministocin gwamnatin Spain, kana ya sha ruwan caccaka a dandalin sada zumunta daban-daban.
Sai dai a yayin da ake wannan caccakar, ’yar wasan ta fito ta nuna cewa ba komai bane wannan sumba da aka yi mata illa tsabar nuna farin ciki da kauna mara misaltuwa.