Shugaban INEC ya yi barazanar maka PDP a kotu kan zargin ɓata masa suna

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), Mahmood Yakubu, ya shawarci jami’an Jam’iyyar PDP da su guji aibata shi a kafafen yaɗa labarai ko kuma su ya ɗauki matakin shari’a.

Babban Sakataren Yaɗa Labaran Shugaban na INEC, Mr Rotimi Oyekanmi, shi ne ya bayyana haka a matsayin raddi ga kiran da PDP ta yi na sai dai Farfesa Yakubu ya sauka daga muƙaminsa.

PDP ta buƙaci Yakubu ya sauka daga muƙaminsa a matsayinsa na mai gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan Majalisar Tarayya, saboda zargin tafka maguɗi.

Lamarin da Yakubu ya ce idan akwai abin da PDP ba ta gamsu da shi ba kamata ya yi ta tafi kotu maimakon mita a kafafen yaɗa labarai.

Ya ce PDP ba ta da ƙwaƙƙwarar hujjar da za ta tabbatar da duka zargin da take yi a kan Yakubun.

“PDP ta gaza gabatar da hujjar da za ta tabbatar da zarge-zargen da ta ƙaƙaba wa Yakubu na saɓa Dokar Zaɓe ta 2022 da dokin INEC….” in ji Oyekanmi.