Shugaban kamfanin Blueprint ya zama magatakardar kungiyar masu gidajen jarida ta kasa

Kungiyar masu gidajen jaridu ta kasa wato NPAN ta yi taronta na shekara a ranar 8 ga watan Disamba a sabuwar sakatariyarta da ke birnin Ikko, in da ta zabi sabbin shugaba da sauran yan kwamitin zartarwa na kungiyar.

Wadanda aka zaba sun hada da:

Mallam Kabiru Yusuf na kamfanin jaridar Trust Media Limited a matsayin shugaba.

Madam Maiden Ibru kamfanin Guardian a matsayin mataimakiya

Mohammed Idris na kamfanin Blueprint  a matsayin Sakatare

da kuma: Mr Wale Edun shugaban kamfanin the Nation a matsayin ma’aji.

Sauran sun hada da Mista Nwaduito Iheakanwa na kamfanin Champion a matsayin Sakataren yada labarai

da

Fidelis Anosike na kamfanin Daily Times a matsayin mataimakin sakatare

Mista Ray Ekpu a mukamin jami’i na musamman

Sam Nda Isaiah shima a matsayin jami’i na musamman

da kuma Dennis Sami shi ma a matsayin jami’i na musamman

An kuma nada Yarima Nduka Obaigbena, Segun Osoba tare da Sam Amuka a matsayin iyayen kungiya.

Taron ya samu halartar manyan yan jarida irinsu: Mista Sam Amuka na jaridar Vanguard, Olusegun Osoba, tsohon gwabnan jihar Ogun, kuma shugaban majalisar jagoranci ta kwalejin horon yan jarida ta kasa, da tsohon shugaban kungiyar Mista Ray Ekpu.

Daga karshe, Kungiyar ta tattauna akan halin da aikin jarida da kuma kasa ke ciki, ta kuma amince da:

Saboda shigar giza gizan da fasahar zamani ke yiwa aikin jarida akwai bukatar majalisar zartarwa ta dau matakan kawo sauyi. Saboda hakan na naso a dabi’ar karatun jarida da kuma tattalin arzikin kasa.

Akwai bukatar hukuma ta lura da irin gudunmawar da jarida ke bayarwa ta fannin ilmi da wayar da kai, ta daukewa jaridun wasu nauyaye-nauyayan kudade da aka daura musu.

Kungiyar ta lura da yadda hukumomi ke yi wa yancin labarai da jaridu hawan kawara, dan haka akwai bukatar a dau mataki kamar yadda sharia ta tanada, akan duk wani yunkuri na dakile wannan yanci na yan jarida. “Kowa ya san akwai yancin zanga zanga a kasa, dan haka ya zama wajibi gwamnati ta tabbatar ba a hana kowa wannan yanci ba”

Kungiyar mu ta dau ilmin yada labarai da muhimmanci, dan haka za ta bayar da gudunmawar ta wurin cigaban kwalejin aikin jarida ta kasa.  Domin ta tabbatar da kwalejin ta sauke nauyin da aka daura mata.

Ya zama wajibi, gwamnatin tarayya ta zage dantse wurin, kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ta hanyar hana ta’addanci da satar mutane da yayi kamari a kasar. 

Mu na kuma kira ga gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye akan batun samar da rigakafin cutar Corona, ta yi kokari ta samo rigakafin ta duk hanyar da ta dace, domin kare mutanen ta daga wannan cuta.

Sa hannu

Malam Kabiru Yusuf

Shugaba

Mohammed Idris

Sakatare

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*