shugaban kamfanin jaridar leadership ya kwanta dama

Shugaba Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan marigayi, Sam Ndah Isiah.

Shugaban dai ya bayyana Mista Sam a matsayin dan’uwa kuma abokin tafiya.

Sakon a ya kara da cewa, wannan rashi ba iyalan sa kadai ya shafa ba, har ma daukacin yan jarida da kuma al’umar kasa gaba daya.

Sakon ya kare da cewa “ba shakka, kasar nan ta yi rashin gwargwazo, abin koyi”

Mista Sam Ndah dai kafin rasuwar tasa, shine shugaban kamfanin jaridar leadership, kuma ya taba tsayawa takarar shugaban kasa, karkashin tutar jam’iyyar APC a shekarar 2015.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*