Shugaban majalisa ya buɗe wasu ayyukan sanata a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan jiya Alhamis ya buɗe wasu ayyukan da Sanata Dakta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi mai wakiltar gundumar Kebbi ta arewa ya aiwatar a garin Argungu.

Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da titin ‘Sanata Adamu Aliero’ wanda ya tashi daga mahaɗar babban titin Sakwato zuwa cikin anguwar Gazange, shugaban majalisar dattawan ya yaba wa Sanata Dakta Yahaya bisa ga irin wakilcin da ya ke bai wa al’ummar mazaɓarsa, inda ya ce, yadda mutanen da ya ke wakilta a majalisar dattawa shaida ne saboda a fili ya ke ƙarara kowa ya gani da idonsa haka su ma da suka a zauren majalisa shaida ne bisa ga irin gudummawar da ya ke baiwa a kowane zama a majalisa.

Ya ƙara da cewa, irin waɗannan mutanen su ne ya kamata a riƙa bai wa shugabanci da kuma wakilcin al’umma saboda mutane masu riƙon amana.

Ya ci gaba da cewa, yanzu Sanata Dakta Yahaya Abubakar Abdullahi shi ne ya biyo al’ummar mazaɓarsa bashi saboda ba shakka ya isar da saqon al’ummar mazaɓarsa kuma sun shaida da haka.

Da ya ke zantawa da wakilinmu, shugaban kwamitin gudanarwa na Sanatan Alhaji Aliyu Gandu Augie ya bayyana cewa, Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi ba wakiltar ’yan jam’iyyar APC kaɗai ya ke yi ba ko na mazaɓarsa kaɗai ba, a’a yana wakiltar al’ummar Jihohi ne saboda har wajen mazaɓarsa ya yi ayyuka na a zo a gani kuma masu inganci.

Waɗansu daga cikin titunan da aka qaddamar dai sun haɗa da titunan cikin Kwalejin ilmi ta Adamu Augie, Tintin da ya tashi daga Subtreasury zuwa low-cost, titin hukumar zaɓe zuwa gwazange.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *