Shugaban Nijeriya ya ƙaddamar da sabon sashen sauka da tashin jiragen sama da Sin ta tallafa wajen ginawa a Legas

Daga CMG HAUSA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabon sashen sauka da tashin jiragen sama, a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed dake birnin Ikon jihar Lagos.

Yayin ƙaddamarwar, shugaba Buhari ya ce an tsara sabon sashen ne, ta yadda zai riƙa karɓar fasinjoji miliyan 20 a duk shekara, yayin da kuma zai samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye har 3,000, da kuma wasu guraben da ba na kai tsaye ba.

Shugaban ya ƙara da cewa, kammalar aikin ya buɗe wani sabon babi na sufurin jiragen sama, mai cike da tsaron lafiya da dukiyoyi, da gamsar da matafiya dake zirga-zirga ta jiragen sama.

Shugaban ya kuma bayyana ƙarfin gwiwar sa, game da ikon sabon sashen filin jirgin na samar da gudummawar raya harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasar.

Aikin dai daya ne daga irin sa guda 4, da aka gudanar a manyan filayen jiragen saman Najeriya, a wani mataki na ƙara zamanantar da sufurin sama, da kyautata hidimomin sa ga matafiya. Sabon sashen dai ya kunshi wuraren karɓar fasinjoji 66, da na jami’an hukumar shige da fice masu tarbar fasinjoji 16, da na masu lura da fasinjoji masu fita 28. Sai kuma sashen tantance fasinjoji ta fuskar tsaro guda 8, da kuma wasu karin sassan na daban.

Fassarawa: Saminu