Shugaban PDP da aka yi wa dukan kawo wuƙa a Ebonyi ya mutu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban jam’iyyar PDP a Ƙaramar Hukumar Ezza ta arewa Peter Nweke, ya mutu.

Nweke ya mutu ne sakamakon raunukan da ya ji bayan wasu da ake zaton ’yan dabar siyasa ne sun farmake shi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris yayin zaɓen gwamnoni da na ’yan majalisar jihohi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ebonyi, Onome Onovwakpoyeya, ta tabbatar da mutuwar Nweke a ranar Lahadi, 19 ga watan Maris.

Ta ce, an yi wa Nweke dukan tsiya sannan aka kwashe shi zuwa asibiti a cikin mawuyacin hali inda daga bisani likita ya sanar da mutuwarsa.

Onome ta ce, rundunar ’yan sandan ta ƙaddamar da bincike a kan mutuwarsa da nufin kamawa da hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin.

Ƙanin mamacin, Samson Nweke shima ya tabbatar da batun mutuwar tasa.

Ya bayyana cewa, ’yan daba ne suka yi wa yayansa duka har sai da ya rasa inda kansa yake.

Ƙanin Nweke ya ce, ’yan daban riƙe da bindigogi ƙirar AK-47 sun farmaki rumfar zaɓen yayansa da ke PU 10, gundumar Ogboji, ƙaramar hukumar Ezza ta arewa, jihar Ebonyi.

A cewarsa, ’yan daban sun zo ne a kan babura biyu sannan suka riƙa jansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *