Shugaban Rundunar Sojoji, Ibrahim Attahiru ya rasu a haɗarin jirgin sama a Kaduna

Daga WAKILINMU

Wani jirgin saman sojojin Nijeriya ɗauke da Shugaban Rudunar Sojoji, Ibrahim Attahiru tare da wasu jami”an rundunar,. ya yi haɗari.

Duk da dai babu ciikakken bayani game da haɗari, amma dai bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna babu wanda ya tsira a haɗarin.

A cewar majiyar MANHAJA, haɗarin ya auku ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin Juma’a a babban filin jirgin saman Kaduna sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka samu.

Rundunar Sojan Sama ta Nijeriya (NAF) ta tabbatar da aukuwar haɗarin.

Sanarwar da rundunar ta fitar wadda ta samu sa hannun Daraktan Sashenta na Hulɗa da Jama’a, Edward Gabkwet, ta ce ba a kai ga tantance musabbabin aukuwar haɗarin ba.


Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Gen Attahiru

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bi sawun ‘yan Nijeriya wajen nuna alhininsa dangane haɗarin jirgin saman da ya yi sanadiyar mutuwar Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Lt. Gen. Ibrahim Attahiru, tare da wasu jami’an soji.

Buhari

A wata sanarwa wadda ta sami sa hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Femi Adesina, Buhari ya bayyana waɗanda suka rasu a haɗarin a matsayin jarumai waɗanda suka rasa rayukansu wajen ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Buhari ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayan da rundunar sojoji da ma ƙasa ɗungurungun.

Baya ga addu’ar saduwa da rahmar Allah da ya yi wa marigayan, Shugaba Buhari ya ce mamatan ba su mutu a banza ba.


Saƙon ta’aziyyar Sanata Bala Ibn Na’Allah kan rasuwar Attahiru

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Sha’anin Rundunar Sojar Sama, Sanata Bala Ibn Na’Allah, ya bayyana kaɗuwarsa kan hadarin jirgin saman da ya ci ran Shugaban Rundunar Sojoji, Ibrahim Attahiru tare da wasu.

Sanata Ibn Na’Allah

Ibn Na’Allah ya ce, “Na kaɗu da samun labarin haɗarin jirgin saman sojan saman Nijeriya samfurin Kingair 350 wanda a cikinsa Shugaban Rundunar Sojoji ya yi tafiya.

“Labarin mutuwar mutumin ƙwarai, Lt Gen Ibrahim Attahiru, ya taɓa ni matuƙa, wanda ya cim na ajalinsa a halin yi wa ƙasarmu aiki.

“A madadin Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Sha’anin Rundunar Sojan Sama na Ƙasa, ina miƙa ta’aziyyarmu ga ƙasa baki ɗaya, da Rundunar Soja da kuma iyalan marigayin dangane da wannan rashi.

“Da fatan Allah Ya jikansa da rahmarSa, Ya sanya Aljanna Firdausi makoma.”


Jerin sunayen waɗanda hadarin jirgin sama ya rutsa da su a Kaduna:

TAWAGAR ATTAHIRU:

  1. LT GEN I ATTAHIRU.
  2. BRIG GEN MI ABDULKADIR.
  3. BRIG GEN OLAYINKA.
  4. BRIG GEN KULIYA.
  5. MAJ LA HAYAT.
  6. MAJ HAMZA.
  7. SGT UMAR.

MA’AIKATA:

  1. FLT LT TO ASANIYI.
  2. FLT LT AA OLUFADE.
  3. SGT ADESINA.
  4. ACM OYEDEPO.