Shugaban Rwanda na fatan ci gaba da bunƙasa alaƙar da ke tsakanin Rwanda da Sin

Daga CMG HAUSA

A kwanakin baya ne, shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagami, ya bayyana yayin wata zantawa ta musamman da wakilin CMG cewa, yayin da ake inganta shirin raya ƙasar Rwanda na tsawon shekaru 20 daga shekarar 2000 zuwa 2020, ƙasar Sin ta taimaka matuƙa a fannonin zamanintar da abubuwan more rayuwa, da kiwon lafiya da ilimi da sauransu.

Muna godiya matuka ga ƙasar Sin. Ƙasar Rwanda za ta kara mayar da hankali wajen samar da ci gaba mai ɗorewa nan da shekaru 30 dake tafe, muna kuma fatan za mu ci gaba da haɗin kai a wannan fanni.

Ya bayyana cewa, nan ba da daɗewa ba, za a gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20, taron dake zama wani babban lamari ga ƙasar Sin.

Muna sa ran haka, bayan wannan babban taro dake tafe, alaƙar abokantaka dake tsakanin ƙasashenmu za ta bunƙasa zuwa babban matsayi.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *