Daga BELLO A. BABAJI
Wani shugaban makarantar Sakandire daga Jihar Zamfara ya samu kyautar lambar yabo na ofishin shugaban ƙasa na gwarzon malami ta shekarar 2024.
A ranar 5 ga watan Oktoban kowacce shekara ne ake bikin ranar malamai ta duniya wanda UNESCO ta shirya da aka fara a shekarar 1994 don yaba wa malamai saboda ƙoƙarinsu na samar da ci-gaba acikin al’umma.
An gudanar da bikin ne a filin taro na ‘Eagle Square’ da ke Abuja wanda Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume ya jagoranta inda shugaban makarantar Sambo Secondary School, Mallam Musa Yahaya da ke Gusau ya lashe kyautar gwarzon malami.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce Malamin ya samu lambar girma da kuma wata sabuwar mota, wanda hakan ya nuna tasirin sanya dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi a Zamfara da Gwamna Dauda Lawal ya yi a watan Nuwamban 2023 don inganta harkar a jihar.
An kuma bai wa sauran malamai kyautuka daga makarantun kuɗi da na gwamnati da suka taho daga sassa daban-daban na faɗin Nijeriya.