Shugaban Zimbabwe ya ƙaddamar da aikin gyara wurin haƙar sinadarin Lithium da kamfanin Sin zai aiwatar

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya halarci bikin ƙaddamar da aikin gyara wurin hakar sinadarin Lithium na Bikita, wanda shi ne irinsa mafi girma a ƙasar.

Kamfanin Sinomine Resource Group na ƙasar Sin ne ya sayi wurin na Bikita a watan Janairun bana, inda yake shirin zuba jarin dalar Amurka miliyan 200 don gyaran sa, da nufin inganta aikin samar da sinadarin Lithium da ƙara samar da aikin yi a yankin.

Shugaba Mnangagwa ya bayyana a gun bikin cewa, gwamnatin ƙasar Zimbabwe na ba da muhimmanci ga kamfanonin Sin da suka zuba jari a ƙasar. Ya ce a shekarun baya-baya nan, kamfanonin Sin da dama sun zuba jari a ƙasar a fannonin ayyukan more rayuwa da haƙar ma’adinai da aikin noma da sadarwa da sauransu, wadanda suke amfanawa masu zuba jarin da kuma yankunan dake samun jarin.

Shugaba Mnangagwa ya ƙara da cewa, yana fatan za a yi amfani da jarin waje ciki har da jarin Sin, don sa kaimi ga ƙasar Zimbabwe wajen harƙar sinadarin Lithium yadda ya kamata, da taimakawa ƙasar wajen cimma burin samun kudi dalar Amurka biliyan 12 daga ɓangaren haƙar ma’adinai a shekarar 2023. Kana yana fatan masu zuba jari za su taimakawa ƙasar Zimbabwe wajen inganta ƙarfin ƙera kayayyaki da bunƙasa masana’antu don ƙara samar da gudummawa wajen samar da makamashi ba tare da gurbata muhalli ba.

Fassarawa: Zainab