Daga BASHIR ISAH
Kwamitin gudanarwa na ƙasa na ƙungiyar kansilolin jam’iyyar APC (NPCF) ya amince da naɗin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa.
Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Hon Muslihu Yusuf Ali, ta bayyana haka ne cikin sanarwar manema labarai da ta fitar mai ɗauke da sa hannnun Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa, Hon Abayomi A. Kazeem da kwanan wata 29 ga Yuli, 2023.
A cewar ƙungiyar, bai wa Ganduje shugabancin jam’iyyar ya yi daidai kasancewar gogaggen ɗan siyasa, ƙwararre wanda ya samar da ɗimbin cigaba a Jihar Kano a zamanin gwamnatinsa.
Daga nan, ƙungiyar ta nuna godiyarta ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu dangane da zaɓa jam’iyyarsu ta APC mutumin ƙwarai a matsayin jagora.
Ganduje ya taki wannan matsayi me biyo bayan murabus da tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi daga kujerarsa shugabancin jam’iyyar.