Shugabannin ƙananan hukumomi sun amfana da bitar Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata – Hon. Fulatan

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban Ƙaramar Hukumar Rogo Hon. Mubarak Basiru Bello Fulatan ya bayyana cewa, taron sanin makamar aiki da hukumar kula da ɗa’ar ma’aikata ta shirya wa shugabannin ƙananan hukumomi da Kansiloli a jihar Kano, da nufin ƙara kawo gyara musamman ga yadda ake cike-ciken nemem bayanai akan yadda zaɓaɓɓu shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli za su gabatar da irin kadarorin da suka mallaka.

Ya ce, a matsayin mutum na zaɓabɓen Shugaban Ƙaramar Hukuma ko Kansila akwai matsala idan ba ka yi wani abu yadda doka ta tanadi ba, zai iya yiwuwa a sami matsala ko bayan ka gama mulki wani abu ya taso, amma yanzu wannan zai sa ka gane abu na daidai da akasin haka.

Fulatan ya ce, waɗannan abubuwa na sanin makama sun ɗauke shi da muhimmanci wajen wayar da kan kansiloli da sauran ma’aikata a matakin ƙaramar hukuma don tabbatar da nasara wajen kiyaye amana da aka ɗora musu don cigaban al’umma.

Ya ce, cike irin waɗannan fom na neman bayanai akan abin da shugaba ko kansiloli suka mallaka zai kawo gyara kuma ko bayan ƙarshen mulki ba wanda zai neme ka ya ce baka yi daidai ba. Wannan hukuma na taimakawa wajen sanya yin abu na daidai don a tabbatar an kiyaye dokaki kamar yadda tsarin aiki da doka ta tanada.

Shugaban na Ƙaramar Hukumar Rogo, Hon.Mubarak Basiru Bello Fulatan ya ce, tun zaɓarsa a kan karagar mulki suna da kyakkyawan fahimta na yin aiki tare da kansiloli da sauran ma’aikata don suna komai tare ba wani bare suna haɗa kai su yi aiki don a sami nasarar Gwamnati gaba ɗaya.

Hon. Mubarak Basiru Bello Fulatan ya bayyana irin haɗin kai da goyon baya da kwamishinan ƙananan hukumomi na jihar kano. Hon. Murtala Sule Garo bisa irin goyon baya da haɗin kai da yake ba su don ciyar da Rogo gaba.

Fulatan ya ce, za su cigaba da yin aiki tuƙuru don tabbatar da tsaro da cigaba da kyautata cigaban al’ummar ƙaramar hukumar Rogo.

Ya kuma ƙara nuna goyon bayansa ga sake zaɓen Hon. Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar APC karo na Biyu na Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *