Shugabannin ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun bayyana jimamin rasuwar Jiang Zemin

Daga CMG HAUSA

Shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da dama, sun aike da wasikun ta’aziya ga shugaban kasar Xi Jinping, inda suka nuna jimami game da rasuwar Jiang Zemin.

A sakon da ya aiko, shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, marigayi shugaba Jiang Zemin ya ba da babbar gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sinawa da kyautata matsayinta a duniya.

Ya kara da cewa, Jiang Zemin tsohon abokin Rasha ne, wanda ya taka muhimmiyar rawa, wajen inganta dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.

Kuma a ko da yaushe yana tunawa da wannan dan siyasa mai kima da fara’a, yana fatan za a isar da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Jiang Zemin da dukkan jama’ar kasar Sin.

Ita ma shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan, ta mika ta’aziyya ga JKS da jama’ar Sin da iyalan Jiang Zemin.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, a nasa sakon ta’aziyyar ya bayyana cewa, marigayi shugaba Jiang Zemin ya tsaya tsayin daka domin kasar Sin ta shiga cikin harkokin kasa da kasa, da sa kaimi ga babban ci gaban tattalin arzikin kasar, da shigar da kasar cikin kungiyar cinikayyar duniya, ya kuma jagoranci Sin wajen karbar bakuncin babban taron mata na duniya karo na hudu dake da babbar ma’ana.

Don haka, a madadin MDD, yana son mika sakon ta’aziyya ga iyalansa da gwamnati da jama’ar kasar Sin.

Haka shi ma shugaban majalisar tarayyar kasashen Turai Charles Michel, ya nuna alhininsa game da rasuwar Jiang Zemin.

Mai fassara: Safiyah Ma