Shugabannin ƙwallon ƙafar Sifaniya sun buƙaci Rubiales ya yi murabus

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na Sifaniya sun yi kira ga shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar, Luis Rubiales da ya gaggauta yin murabus bayan ya sumbaci ‘yar wasa Jenni Hermoso.

Rubiales, mai shekaru 46, ya sha suka sosai bayan da lamarin ya faru bayan kammala wasan ƙarshe na gasar kofin duniya na mata a da Sifaniya ta lashe.

Hermoso, mai shekaru 33, ta ce ba ta amince da sumbar da Rubiales ya yi mata ba.

Tun da farko, masu gabatar da ƙara na Sifaniya sun ƙaddamar da bincike na share fage kan ko lamarin ya kai wani laifi na cin zarafi.

A wani labarin kuma a ranar Litinin, mahaifiyar Rubiales, Angeles Bejar, ta kulle kanta a wani coci, inda ta tafi yajin cin abinci, domin nuna rashin amincewa da yadda aka yi wa ɗanta.

Da yammacin ranar ɗaruruwan mutane ne suka taru a tsakiyar birnin Madrid a zanga-zangar da ƙungiyoyin mata masu rajin kare haƙƙin mata suka kira don nuna goyon bayansu ga Hermoso da kuma nuna adawa da Rubiales.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta dakatar da Rubiales a ranar Asabar, kwana daya bayan da ya dage cewa ba zai yi murabus ba, ya kuma yi ikirarin sai da ‘yar wasan ta amince kafin ya sumbace ta.

UEFA dai ta tuntubi Fifa amma ba ta ce uffan ba saboda lamarin ya faru ne a gasar da Fifa ta shirya, don haka ƙungiyar ta Turai na ganin ya dace hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ta jagoranci binciken.