Shugabannin Afrika sun miƙa kukansu a taron Paris

Shugabannin ƙasashen Nijar Benin da kuma Ghana sun miƙa kokensu ga taron yanayin da ke gudana a birnin Paris kan yadda manyan ƙasashe ke mayar da hankali wajen zuba maƙuden kuɗi a Ukraine ba tare da duba halin da nahiyar Afrika ke ciki ba, koken da ke zuwa a dai dai lokacin da Amurka ta sanar da shirin zuba ƙarin dala biliyan 1 da miliyan 300 don farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar mai fama da yaqi.

Shugabannin ƙasashen na Ghana Benin da kuma jamhuriyyar Nijar yayin jawabinsu gaban taron yanayin wanda ke ci gaba da gudana a birnin Paris na Faransa sun bayyana cewa ba laifi ba ne manyan qasashen su taimaka wa Ukraine amma akwai buƙatar bai wa nahiyar Afrika muhimmanci lura da halin da ta ke ciki na tsananin buƙtar agaji fiye da Ukraine.

Shugabannin uku waɗanda ko a taron asusun IMF da Bankin Duniya da ya gudana cikin watan Aprilu a Washington sai da suka ja hankalin manyan ƙasashe game da matakin da suke ɗauka na fifita buqatun Ukraine akan na Afrika, sun ce akwai matuƙar damuwa kan yadda ƙasashen ke kawar da kai ga halin da Afrikan ke ciki duk tsananin buƙatar agajinta.

Wannan kira na shugabannin Afrika uku da suka ƙunshi Bazoum Mohamed na Nijar da Nana Akufo Ado na Ghana da kuma Patrice Talon na Benin, sun bayyana cewa idan har da manyan ƙasashe za su kwatanta makamancin tallafin da suke turawa Ukraine ga Afrika ko shakka babu da nahiyar ta fice daga wasu tarin matsaloli da suka dabaibaye ta.

Daga farkon faro yaƙin na Ukraine zuwa yanzu ƙasashen yammacin duniya sun alƙawarta sanya kuɗin da ya haura dala biliyan 10 don farfaɗo da ita, dai dai lokacin da hare-haren Rasha ya kassara tattalin arzikinta da koma bayan kashe 30 a ma’aunin GDP.