Shugabannin duniya sun yi na’am da zaɓen Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sabon zaɓaɓɓen shugaban Tarayyar Nijeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yana cigaba da samun tagomashi a duniya ta hanyar karɓar saƙon taya murna daga shugabannin ƙasashen duniya, inda kawo yanzu kusan dukkan manyan ƙasashen duniya masu faɗa-a-aji sun aiko masa da saƙonnin taya murna tare da ba shi tabbacin za su yi aiki tare da shi.

Idan za a iya tunawa, a ranar Laraba, 1 ga Maris, 2023, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ta sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a ranar Asabar, 25 ga Fabrairu, 2023.


Wakilin Blueprint Manhaja, MAHDI M. MUHAMMAD, ya tattaro wasu daga cikin saƙonnin da Asiwaju Bola Tinubu ya samu, kamar haka:

Amurka ta taya Tinubu murna:

Gwanmatin Amurka ta aike da saƙon taya murnar nasarar Bola Ahmed Tinubu a matsayin zaɓaɓɓen shugaban Nijeriya.

A waje guda kuma fadar White House ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankula bayan zarge-zargen maguɗi da matsaloli da aka fuskanta yayin zaɓen.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana saƙon taya murnar ne a lokacin da yake ganawa da takwaransa na Nijeriya Geoffrey Onyeama a wajen taron ƙasashe masu ci gaban masana’antu na G20 da ake yi a birnin New Delhi na qasar Indiya.

A cikin wata sanarwa, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tana sane da ƙorafin ‘yan Nijeriya da wasu jam’iyyun siyasar ƙasar suka bayyana kan damuwarsu game da zaɓen.

Shugaban ƙasar Ghana ya taya shi murna:

Shugaban ƙasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya bi sahun sauran shugabannin ƙasashen duniya domin taya zaɓaɓɓen shugaban Tarayyar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu murna.

Saƙon taya murna na shugaban Ghana na ƙunshe ne a wani saƙon da ya wallafa a shafin na manhajar Facebook a ranar Alhamis, 2 ga Maris, 2023.

Da yake miƙa saƙon taya murna ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasan, Akufo-Ado ya ce, “Nasarar da Tinubu ya samu ya sa gwamnatin APC mai mulki ta qara wa gwamnatin APC ƙarin shekaru huɗu ta ci gaba da mulki, wanda kuma ina fata za a yi nisa domin inganta harkokin mulki, bin doka da oda da kuma yadda tattalin arzikin Nijeriya ke tafiya”.

Akufo-Addo ya kuma yabawa ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP da Labour Party, Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi, bisa jajircewarsu, da yaƙin neman zaɓe.

Ya ce, martanin ’yan takarar da ba su yi nasara ba game da sakamakon zaɓen zai ƙarfafa iyakoki na dimokuraɗiyyar Nijeriya, da kuma ƙarfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya, babbar ƙasar Afirka.

Ƙasar Ingila:

Har ila yau, Firayim Ministan Birtaniya, Rishi Sunak, a ranar Laraba, ya taya Tinubu murnar nasarar lashe zave ta shafinsa na Tuwita.

“Ina taya Bola Ahmed Tinubu murnar nasarar da ya samu a Nijeriya,” in ji Sunak a ranar Laraba.

Sunak ya tabbatar da cewa, “Dangantakar Birtaniya da Najeriya ta kasance mai ƙarfi. Ina fatan yin aiki tare don bunƙasa dangantakarmu ta tsaro da kasuwanci, da buɗe hanyoyin kasuwanci da samar da wadata a ƙasashenmu biyu.”

Faransa:

Haka zalika, shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron ya taya tsohon gwamnan jihar Legas murnar nasarar da ya samu a rumfunan zaɓe.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan gabatar da takardar shaidar lashe zaɓensa.

Ya ce, ya samu saƙonnin taya murna da dama a ciki da wajen Nijeriya, inda ya ambaci shugaban ƙasar Faransa a cikin su.

Da yawa, da yawa daga cikinsu, a gaskiya har zuwa Turai, kasuwannin hada-hadar hannayen jari sun turo min saƙonni da yawa, akwai saƙon fatan alheri daga Macron, Shugaban Faransa,” in ji Tinubu.

Jamhuriyar Nijar:

Shugaban ƙasar jamhuriya Nijar, Mohamed Bazoum, ya bi sahun saran shugabannin ƙasashe duniya wajen taya zaɓaɓɓen shugaban Tarayya Nijeriya muryar lashe zaɓen 2023.