Shugabannin Tarayyar Turai da ke taro a Brussels jiya Litinin sun yi gargaɗin cewa. babu wanda zai yi nasara a yakin kasuwanci da Amurka, inda suka dage cewa za su mayar da martani idan Shugaba Donald Trump ya saka haraji.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, dole ne Tarayyar Turai ta mayar da martani matuƙar shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da barazanar da ya yi na saka wa ƙungiyar haraji.
Macron ya ce, “Idan aka kai mana hari ta fuskar kasuwanci, Turai a matsayinta na mai cikakkiyar ƙarfi da iko dole ne ta tashi tsaye don kare kanta.”
Shugabannin ƙasashe 27 na ƙungiyar EU sun yi tururuwa a babban birnin ƙasar Belgium tare da firaministan Birtaniya da kuma shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO, domin tattaunawa kan ƙoƙarin da ake yi na inganta tsaron Turai da ke fuskantar Rasha mai tsatsauran ra’ayi, a daidai lokacin da shugaba Trump ya bikiro da zancen ƙawayen Amurka su lamushe kuɗaɗe masu yawa.
Saidai shawarar da shugaban Amurka ya yanke na sanya haraji kan Kanada, Meɗico da Chana ya mamaye tattaunawar tare da barazanar da Trump ya yi na kai hari ga EU nan gaba.
Firayim Ministan Poland Donald Tusk, wanda a halin yanzu ƙasarsa ke riƙe da shugabancin EU, ya ce, dole ne a yi mai yiwa domin kaucewa yakin kasuwanci “wanda ba zai haifar da ɗa mai ido ba.”
Trump dai bai boye ƙiyayyar sa ga ƙungiyar ta EU ba, yana mai zarginta da yiwa Amurka rashin adalci a harkar kasuwanci.
Bayan ɗora haraji kan maƙwabtansa na Arewacin Amurka da Chana, Trump ya ninka sau biyu a ranar Lahadin da ta gabata yana mai cewa “tabbas” yana shirin kai hari ga EU a nan gaba.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce takaddamar kasuwanci za ta kasance “ba mai haifar da ɗa mai ido ba ga Amurka, kuma ba za ta yi kyau ga Turai ba,” don haka ya nemi “haɗin kai, da fahimtar juna” wanda ya fi dacewa ga ɓangarorin biyu.
“Muna kuma iya mayar da martani,” inji shi, yana kaucewa tsarin taka-tsan-tsan na al’adar Jamus game da huldar kasuwanci.
Babbar jami’ar diflomasiyyar EU, Kaja Kalas ta ƙara da cewa “Muna buƙatar Amurka, ita ma Amurka na buƙatar mu,” inji babbar jami’ar diflomasiyyar EU, Kaja Kalas, ta ƙara da cewa, “Babu waɗanda za su yi nasara a yaƙin kasuwanci.”
A ranar Lahadin da ta gabata, Hukumar Tarayyar Turai ta ce, za ta mayar da martani “da gaske” idan Trump ya bai ja baya kan ƙudurinsa kanta ba, ta kuma yi tir da matakin da ya ɗauka kan Canada, Meɗico da Chana.
“Haraji na haifar da rushewar tattalin arziki marar dalili, kuma yana haifar da hauhawar farashin kayayyaki, wanda yake da illa ga kowane ɓangare,” inji kakakin hukumar.