Shugabannin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi sun ajiye muƙamansu

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Bayan wani zama na gaggawa da shugabannin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi suka yi a jiya Alhamis, sun yanke shawarar ajiye muƙamansu.

Wannan yana ƙunshe a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Shehu Muhammed Yauri, sakataren yaɗa labarai na majalisar. Sai dai takardar ba ta bayyana dalilin ajiye muƙaman da suka yi ba.

Shugabannin majalisar dokokin da suka sauka daga kan muƙaman nasu dai sun haɗa da Mataimakin Kakakin  Majalisar da Mai Tsawatawa da mataimakinsa zuwa shugabannin masu rinjaye da marasa rinjaye da mataimakansu.

Har wa yau dai, ’yan majalisar sun nemi gwamnan jihar, Atiku Bagudu, da ya gurfana gaban majalisar yau Juma’a, 27 ga Janairu, 2023, don ya yi bayanin inda ya kai Naira Billiyan 18 da ya karɓo daga hannun Gwamnatin Tarayya, waɗanda su ma ba su yi cikkakken bayani kan hakan ba.

A cikin takardar mai ɗauke da sa hannun Magatakardan Riƙo na Majalisar, Suleiman Shamaki, sunayen mambobi 20 daga cikin 24 na majalisar ne a kai, waɗanda kuma suka rattaɓa hannu a kai.

Wakilin Manhaja na Jihar Kebbi ya ruwaito cewa, gwamnatin jihar ta Kebbi ta amshi kuɗaɗe daban-daban daga hannun Gwamnatin Tarayya kamar haka:

Naira Biliyan 890 na kaso daga Gwamnatin Tarayya a 2015

Naira Biliyan 35 na IGR daga 2015 zuwa yanzu

Naira Biliyan 20 na kuɗin Paris Kulab

Naira Biliyan 14 na Shirin Noma na Anchor Borrowers

Naira Biliyan 15 na Rancen Kuɗi na ‘bail out’

Naira Biliyan 17 da aka sayar wa Gwamnatin Tarayya filin jirgin sama na Ambursa

Biliyoyin Naira na haɗakar asusun jiha da ƙananan hukumomi

Kimanin Naira Biliyan Up 10 na tallafin Bankin Raya Afrika (AfDB, Ƙungiyar Tura (EU) da sauran cibiyoyin duniya

Kuɗaɗen tallafin annobar cutar Korona
Kimanin Naira Biliyan biyu na tallafin manoma.