Shugabannin Sin da Argentina sun aike da wasiƙar murnar buɗe dandalin musayar al’adu tsakanin ƙasashen biyu

Daga CMG HAUSA

A yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping da takwaran aikinsa na ƙasar Argentina Alberto Fernández sun miƙa wasiƙar murnar buɗe taron dandalin tattaunawa kan musayar al’adu tsakanin ƙasashen biyu.

A cikin wasiƙar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 50 da ƙulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Argentina.

A cikin rabin karnin da ya gabata, dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu ta himmatu wajen tinkarar ƙalubalen da ƙasashen duniya suke fuskanta, kana ta zama abin koyi na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa a fannonin hadin gwiwa da samun bunƙasuwa tare.

Xi Jinping ya yi fatan mahalarta taron, za su yi musayar ra’ayoyi da cimma daidaito don sa ƙaimi ga raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da Argentina, kana za su ba da gudummawa wajen gina al’ummar Sin da Latin Amurka mai kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani.

A nasa ɓangare, shugaba Fernández ya bayyana a cikin wasiƙarsa cewa, ƙasashen biyu sun yi haɗin gwiwa har na tsawon rabin ƙarni, kuma ya yi imanin cewa, ƙasashen biyu za su samu kyakkyawar makomar bai ɗaya a nan gaba.

Kana haɗin gwiwar dake tsakanin kafofin watsa labaru na ƙasashen biyu, ta sa ƙaimi ga fahimtar juna tsakanin jama’ar ƙasashen biyu.

Mai fassara: Zainab