Shugabannin Sin da Congo (Kinshasa) sun aike wa juna saƙon murnar cika shekaru 50 da ɗora hulɗar ƙasashen biyu kan hanyar da ta dace

Daga CMG HAUSA

Yau Alhamis ne shugaba Xi Jinping na ƙasar Sin, da takwaransa na ƙasar Congo (Kinshasa) Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, suka aikewa juna sakon murnar cika shekaru 50 da ɗora hulɗar da ke tsakanin ƙasashen 2 kan hanyar da ta dace.

A cikin saƙonsa, Xi ya nuna cewa, a rabin ƙarnin da ya gabata, ƙasashen 2 sun raya hulɗa a tsakaninsu yadda ya kamata, sun kuma rika zurfafa dankon zumunci a tsakaninsu.

A shekarun baya, ƙasashen biyu sun kafa hulɗar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, kuma haɗin gwiwarsu ya haifar da sakamako mai yawa, kuma hakan ya amfani al’ummomin ƙasashen biyu.

Xi ya kara da cewa, yana dora muhimmanci kan raya dangantaka a tsakanin ƙasar Sin da ƙasar Congo (Kinshasa), yana kuma son yin ƙoƙari tare da shugaba Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, wajen yin amfani da damar cika shekaru 50 da ɗora hulɗar ƙasashen biyu a kan hanyar da ta dace, domin zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da inganta haɗin gwiwarsu a fannin aiwatar da shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”, da kuma bude sabon babi na bunƙasar hulɗar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

A nasa ɓangaren, Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo ya ce, a cikin shekaru 50 da suka wuce, ƙasarsa da Sin sun bunƙasa hulɗa a tsakaninsu yadda ya kamata ba tare da kasala ba.

Yana kuma fatan kara zurfafa dankon zumunci a tsakanin ƙasashen biyu, da ƙara azama kan samun sabbin sakamako wajen bunkasar hulɗar abokantaka a tsakanin ƙasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, a ƙoƙarin kawo wa jama’ar ƙasashen biyu alheri.

Mai fassara: Tasallah Yuan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *