Shahararrun ‘yan bindiga, Abu Radde da Umar Black, sun miƙa wuya tare da miƙa makaman su a ƙaramar hukumar Batsari, Jihar Katsina. A yayin wannan lamarin, an ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su, ciki har da maza uku, mata takwas, da yara huɗu.
Wannan lamari ya zo ne a matsayin wata babbar nasara a yaƙi da ‘yan bindiga a yankin.
Taron miƙa wuyan ya gudana a ranar 19 ga Janairu, 2025, a cikin yanayi na gaskiya da tsaro. Manyan jami’an tsaro, ciki har da wakilan sojoji, sun halarci wannan bikin tarihi domin tabbatar da sahihancin miƙa makaman. ‘Yan bindigar sun miƙa bindigogi huɗu kirar AK47, waɗanda yanzu ke hannun rundunar 17 Brigade na soja.
A cewar rahotanni, wannan miƙa wuya na daga cikin matakan da ake ɗauka domin tabbatar da cikakken tsagaita wuta tare da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda aka yi garkuwa da su.
Jami’an tsaro na Operation FASAN YANMA sun taka muhimmiyar rawa wajen cimma wannan nasara ta musamman, wadda ta fara kawo sauƙi ga al’ummar Katsina.
Wannan ci gaban ya zama alamar sabuwar rayuwa ga mutanen Katsina, waɗanda suka daɗe suna fama da fargabar ‘yan bindiga. Miƙa wuya Abu Radde da Umar Black ya nuna jajircewar jami’an tsaro da kuma yadda suke aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da tsaron yankin.