Shugabar Ƙungiyar Matan APC ta ba da shawarar saka mata a FEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugabar Ƙungiyar Mata ta Jam’iyyar APC ta Ƙasa, ta yi kira da a saka mata da yawa a Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC).

Edu ta yi wannan kiran ne a wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ranar Laraba a Kalaba yayin bikin tunawa da ranar mata ta duniya ta 2023 (IWD).

NAN ta ruwaito cewa, ana amfani da ranar ne domin nuna nasarorin da mata suka samu, da wayar da kan mata game da nuna wariya da kuma ɗaukar matakin magance daidaiton jinsi.

Taken ranar shine “Ƙirƙirar Fasaha don Daidaiton Jinsi.”

Edu, wanda tsohon kwamishinan lafiya ne a Kuros Riba, ya ce ya kamata a lura da al’amuran matan Nijeriya, kuma su kasance a sahun gaba wajen cigaban jihohi da gwamnatin tarayya.

Tana fatan cewa a shekarar 2023, za a ba wa mata da yawa ƙarfin kuɗi tare da aiwatar da kashi 35 cikin 100 na ingantacciyar aikin a faɗin hukumar.

“A wannan sabuwar gwamnati muna buƙatar mata da yawa a Majalisar Zartarwa ta Tarayya kuma dukkannin hukumomin tsaro na buƙatar su zama mata kashi 35 cikin 100.

“Har ila yau, muna buƙatar shiga tsakani da shirye-shirye daga Gwamnatin Tarayya; muna buƙatar kason da aka sadaukar musamman ga mata.

“Kwarewa dole ne ya zama abin dubawa, muna buƙatar mata masu iya aiki, ƙwarewa kuma za su iya wakilci; muna da su da yawa a cikin al’umma,” inji ta.

Ta ce, nan ba da jimawa ba za a kuɓutar da kwamishinan harkokin mata na Kuros Riba, Dakta Gertrude Njar, yayin da ake ƙoƙarin kuɓutar da ita lafiya.

Victoria Emmah, Babban Darakta na gidauniyar Neighborhood Care Well, ta ce, IWD a jihar ya kasance abin bakin ciki saboda sace Njar.

Emmah, wadda ƙungiyarsa ta kwashe sama da shekaru 20 tana kula da mata da yara, ta ce yau makonni biyar kenan da sace Njar.

“Har sai Nijeriya ta gane cewa mata ba wai kawai ana nufin su kasance a ɗaki ba ne kawai, amma sai don su kawo dabaru masu ma’ana don magance matsalolin cigaba domin mu yi samu cigaba kamar sauran ƙasashe.

“Ya kamata a bar mata su riƙe iko kamar Farfesa Dora Akunyili, Ngozi Okonjo-Iweala, Oby Ezekwesili da sauran mata da dama da ke jagorantar manyan kamfanoni a halin yanzu sun tabbatar da cewa za mu iya yin hakan.”