Shugabar gamayyar ƙungiyoyin mata Jihar Kebbi ta sha alwashin haɗa kan mata

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Sabuwar shugabar gamayyar ƙungiyoyin mata ta ƙasa reshen jihar Kebbi, Hajiya Halima Hassan, ta ƙuduri aniyar haɗa kan matan Jihar Kebbi, domin bunƙasa tattalin arzikinsu.

Ta yi wannan bayani ne jiya Alhamis a garin Argungu lokacin da ta ke zantawa da wakilin jaridar Blueprint Manhaja.

Ta ce ya zama wajibi ga mata da su tashi tsaye wajen haɗa kai ta hanyar ɗabbaƙa ƙungiyoyin mata ta yadda za su samu nasarar samun duk wani shiri na tallafi tun kama daga na sana’o’i ya zuwa neman haƙƙinsu. 

Hajiya Halima Hassan ta ce an kafa wannan ƙungiyar tun shekarar 1958 kuma kawo yanzu akwai ƙasashe goma sha shida da wannan ƙungiyar ke aiwatar da ayyuka na ƙungiyoyin mata, saboda haka ba za a bar su a baya ba su ma za su tashi tsaye wajen wayar da kan mata ta hanyar bayyana musu muhimmancin ire-iren waɗannan ƙungiyoyin.

Ta yi kira ga ƙungiyoyin mata daga matakan ƙananan hukumomi da su yi rajista ga wannan ƙungiyar domin cin moriyar shirye-shiryen gwamnatin jiha da tarayya da kuma na ƙungiyar.

Ta kuma yaba wa Uwargidan gwamnan jihar Kebbi Dr. Zainab Shinkafi Bagudu da gwamnatin jihar bisa ga goyon bayan da ta ke bai wa ƙungiyoyin mata da kuma samun tabbacin bayar da kulawa da tallafi ga ƙungiyoyin mata a jihar.