Shugabar WTO ta iso Nijeriya, za ta gana da Buhari

Sabuwar Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO) Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta iso Nijeriya inda ake sa ran za ta shafe mako guda.

Daga bayanan da Manhaja ta kalato, kai ziyara ga Shugaba Muhammadu Buhari na daga cikin harkokin da Ngozi za ta aiwatar domin nuna godiyarta ga irin rawar da Buhari ya taka wajen ganin ta sami ɗarewa sabon muƙamin nata.

Okonjo-Iweala ta ce yayin ziyarar tata, za ta tattauna da Shugaba Buhari tare da sauran masu ruwa da tsaki game da irin tanadin da WTO ta yi wa tattalin arzikin Nijeriya a matsayinta na shugabar hukumar.