Silar shiga ta cikin marubutan ‘Labarina’ – Saddiƙa Habib Abba

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

Rubutu wani abu ne da masu yin sa su ke samun damar isar da sakon su ga Jama’a yadda za su yaɗa manufar su walau ta ɓangaren addini ko kuma ɓangaren al’ada, da ma fanoni daban daban na rayuwa. Saddiƙa Habib Abba tana cikin Marubutan wannan lokacin da su ke da burin faɗakar da jama’a ta ɓangaren zamantakewar rayuwar su ta yau da kullum, kuma tana ɗaya daga cikin marubutan da Allah ya yi wa baiwar yin rubutun ta kowanne ɓangare. Domin kuwa marubuciyar labarin Hikaya ce, kuma marubuciya ce a kan al’amuran yau da kullum, sannan marubuciyar wasan kwaikwayo ce, wato rediyo drama, sannan kuma jigo ce a cikin marubutan labari a masana’antar finafinai ta Kannywood. A cikin tattaunawar su da wakilin mu fitacciyar marubuciyar ta bayyana mana yadda ta fara harkar rubutu da kuma yadda ta zama fitacciyar marubuciya ba tare da ta fitar da littafi ko guda ɗaya ba kamar yadda aka san marubutan ƙasar Hausa da yin hakan, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:

Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
To Ni dai suna na Saddiƙa Habib Abba. An haife ni a garin Kano kuma a Unguwar Gwammaja. Na yi karatuna na Alƙur’ani Mai Girma a ‘Khlafaurrashidun Islamiyya’ a nan na samu saukar Alƙur’ani Mai Girma a 2009. Sannan na yi karatuna na ‘Nursery’ zuwa ‘Primary’ a ‘Command Childrens School’ Bukabu Barrack Kano. Bayan na kammala na tafi ‘Kings College’ Kano na yi ‘Secondary School’ ɗina har na kammala, yanzu haka ni ɗaliba ce a Jami’ar Bayero, ina karanta ‘Mass Communication’.

Rubutun ki ya sha Bamban da sauran na marubuta waɗanda su ke yin rubutun littattafai, ke sai ya zama kin yi fice a harkar rubutun amma sai a ke ganin ba ki taɓa fitar da littafi ba kamar yadda aka san marubutan mu na Hausa da yin hakan.
To, haka ne domin ni ban fara da rubutun littattafi ba wanda zan ce na fitar da shi a matsayin littafin da na rubuta na fitar da shi kasuwa duk da na so na yi hakan, amma dai abin da ya faru shi ne a daidai lokacin da shigo harkar rubutun, kasuwar littafin ta yi ƙasa saboda haka ina da littattafan da na rubuta amma yanayin kasuwar bai ba ni damar na buga su ba. Amma da ya ke harkar tana da faɗi sai na ɗauki wani ɓangaren don haka sai na duba na ga me ya kamata na yi da basirar da Allah ya ba ni domin isar da saƙo na ga Jama’a, don haka sai na ga harkar fim tana tafiya don haka sai na koma rubutun labarin fim bayan na samu shawarwari daga waɗanda suka daɗe a cikin harkar fim ɗin.

Amma duk da haka wani lokacin kina wasu rubutun da suka shafi al’amuran yau da kullum kamar gajerun labarai ko ta ya ya ki ke yin amfani da su?
E, waɗannan na kan tura ana sakawa a jarida ne domin amfanin jama’a domin na kan tsaya na kalli me ya ke damun jama’a lokacin, sai na faɗi yadda ya ke da kuma yadda za a magance shi.

Amma dai yanzu ana ganin kamar aikin ki ya fi karkata ga rubutun labarin fim.
E gaskiya haka ne, amma ni da farko rubutun littafi na fi sha’awa to amma da na duba yadda kasuwar take kuma da shawarar da na samu daga cikin wasu ‘yan fim ɗin kamar Usman Mu’ azu da Nazifi Asnanic to daga nan sai na faɗa rubutun labarin fim.

Da rubutun qirqira da kuma na al’amuran yau da kullum da ki ke yi ana sakawa a jarida wanne ki ka fi so?
Gaskiya ni kaina na fi son na jarida saboda duk lokacin da na yi ina samun saƙonni da kuma addu’a daga wajen mutane a duk faɗin ƙasar nan kuma wasu suna cewa saboda karanta rubutun nawa sun samu warware wata matsala da su ke da ita wasu kuma su ce rubutun nawa ya canza musu rayuwarsu, don haka ina jin daɗin hakan sosai.

Kamar rubutun ki na soshiyal midiya ta ina ki ke cin gajiyarsa?
To ka san komai yana tafiya da zamani don haka idan na yi ana saya ne ana karanta shi a YouTube, to gaskiya shi ma ina jin daɗin sa saboda yadda na ga mutane suna bibiyar shafukan da a ke saka rubutun nawa.

Kamar a ɓangaren rubutun labarin fim kina rubutun ki a kowane ɓangare ne ko dai a ɓangaren ɗaya ki ka tsaya?
To ka san zamani shi ya ke tafiya da komai don haka rubutun fim ɗin ma akwai fannoni da dama kamar ɓangaren labarin fim da na rediyo drama ka ga ai rubutun da na fi sha’awar sa shi ne na littafi amma na kan duba yadda zan samu abin biyan buƙatar yau da kullum don haka ne ma na fi mayar da hankali na kan rubutun labarin fim.

Za mu so ki faɗa wa masu karatun mu wasu labarun da ki ka rubuta wanda aka yi fim ɗin su.
Ai da ya ke suna da ɗan yawa wasu ma na manta su, amma dai kaɗan daga cikin su akwai rubutun labarin rediyo drama na Shugabanci da ‘Rainon Ɗan’adam’ kuma ina cikin marubutan fim mai dogon zango na ‘Labarina’ wanda a ke haskawa a tashar Arewa 24, akwai ‘Daren Farko’, ‘Ƙarfen Ƙafa’, ‘Auri Saki’, da dai sauran su.

To ya aka yi ki ka samu kan ki a cikin marubutan ‘Labarina’ duk da ba da ke aka fara? ba?
To da farko dai zan yi godiya ga Allah, domin shi ne ya ke ƙaddara komai a lokacin da ya so, don ni kaina ban san zan samu kaina a cikin marubutan ba, duk da ya ke tun lokacin da aka fara haska fim ɗin Labarin ya na burge ni kuma na ji a raina zan iya bayar da tawa gudummawar a cikin sa amma dai ban sanar da kowa ba, sai kawai wata rana mun je gidan Naziru Sarkin Waƙa muka haɗu da Malam Aminu Saira ya tambaye ni ko ina da wani labarin da zai saka a YouTube? To daga nan sai Nasiru Gwangwazo ya kira ni a waya wata rana da safe ya ke cewa zan yi masa wani rubutu, don mun yi magana da shi kusan sa’o’i biyu a waya a lokacin, har ya ke cewa amma rubutun labarin na ‘YouTube’ ne, sai ya ce za mu haɗu da shi a Zoo Road. To a lokacin za a fara rubutun ‘Labarina’ kashi na uku da na huɗu, to sai ya ce Malam Aminu Saira zai kira ki a waya, to bai kira ni ba, sai wata rana ya ke cewa da ni za ki yi rubutun Labarina? Sai na ce me zai hana ni yi. To na san dai Nasiru Gwangwazo shi ne silar shiga ta cikin rubutun Labarina, saboda na san shi ne ya bai wa Aminu Saira cikakken ƙwarin gwiwa a kaina kuma har ya yarda dari bisa dari har ya ji ma zai iya ba ni. Bai dai faɗa mini ba, don ka san shi Gwangwazo ba mutum ne da idan ya yi maka abu zai zo ya rinƙa faɗa ba. Amma dai hakan ce ta faru har Malam Aminu Saira ya shigo da ni cikin rubutun Labarina. To gaskiya babu abin da zan iya cewa sai dai Allah ya saka da alheri don Gwangwazo shi ne silar shiga ta rubutun ‘Labarina’.

Su waye suka zama silar samun nasarar ki a rubutu?
To gaskiya suna da yawa, amma dai kamar jigo dai zan iya cewa mutane uku ne suka zamar mini jigo. A ɓangaren rubutun fim to gaskiya Balarabe Murtala Bahru shi ya fara ba ni taimako, saboda shi ne ya fara duba rubutun da na yi, ya ɓata lokacin sa ya karanta har ya ba ni gyara kuma ya ƙara mini ƙarfin gwiwa cewa zan iya, gaskiya ba zan manta da shi ba. Sai kuma rubutun rediyo drama shi kuma wannan Nasiru B. Muhammad shi ne ya koya mini yadda a ke yi to ya ba ni taimakon da ba zan manta da shi ba. Sai kuma Nasiru Gwangwazo wanda zan iya cewa ma kamar shi ne jigo a cikin harkar rubutun don duk in da na kai ga matsayi a duniyar rubutu, to shi ne ya zamo sila, domin shi ne ya ke ɓata lokacin sa ya na koyar da ni abubuwan da ya kamata na yi, kasancewar sa tsohon marubci da ya san harkar, kuma duk abin da ya shigar mini duhu idan na kira shi zai tsaya ya saurare ni kuma ya yi mini cikakken bayani yadda zan gamsu, don haka ba zan taɓa mantawa da gudummawar da ya ba ni ba, kuma ina roƙon Allah kamar yadda na shiga harkar nan babu wanda ya yi mini baƙin ciki ko ƙyashi, to ni ma Allah ya sa mutane su amfana da abin da na koya don na samu na koyar da su yadda su ma za su amfana da shi nan gaba, kuma a yanzu ma akwai waɗanda na fara koya wa, ina fatan za su ci gajiyar abin nan gaba kamar yadda na ke cin gajiyar abin a yanzu.

To ganin daman kina da burin bayar da ta ki gudummawar sai kuma aka gayyace ki a matsayin wadda za ta yi aikin rubutun ya ki ka ji a lokacin?
A gaskiya na ji daɗi sosai saboda abin da ya ƙara ba ni ƙarfin gwiwa shi ne rubutun ya bambanta da wanda na saba yi don haka ma da farko na yi ta fargaba kada na je na kasa, amma dai da na mayar da hankali sai aikin ya zo mini cikin sauƙi, kuma Alhamdu lillah an yaba da rubutun da na yi.

A fanin rubutu wane burin ki ke da shi?
Gaskiya ina son na yi rubutun da duk duniya za ta sanni kuma ya zama mutane sun amfana da shi a rayuwar su ta duniya da lahira kuma ina so na yi fice ya zama duk duniya an san suna na a matsayin marubuciyar da ta ke yin rubutu mai kyau da ma’ana

Me ya fi ɓata miki rai a cikin harkar ki ta rubutu?
Abin da ya fi ɓata mini rai shi ne na yi rubutu wajen aiki a canza mini ma’anar sa wannan abin ya fi komai ɓata mini rai kuma ya fi zama ƙalubale a cikin harkar rubutun da na ke yi

Menene saƙon ki na ƙarshe?
Saƙo na na ƙarshe dai godiya ce ga duk waɗanda suka taimaka mini da shawarwari da kuma koya mini yadda zan tsara rubutun har na kai ga wannan matakin musamman Balarabe Murtala Bahru da sauran su da dama ina yi musu fatan alheri.

To madalla mun gode.
Nima nagode sosai.