Sin da ƙasashen Afrika masu magana da Faransanci sun shirya taro ta kafar bidiyo game da dimokuraɗiyya

Daga CMG HAUSA

A jiya Talata, ƙasar Sin ta gudanar da taron ƙarawa juna sani ta kafar bidiyo da ƙasashen Afrika 22 masu magana da yaren Faransanci mai taken “Bincike da amfani da demokuraɗiyya a majalisun dokokin ƙasashen Sin da Afrika”.

Ding Zhongli, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin wakilan jama’ar ƙasar Sin (NPC) ya halarci bikin ƙaddamar da taron na kwanaki biyu inda ya ba da wani jawabi.

Yayin ganawar

Mr. Ding ya bayyana cewa, majalisar NPC a shirye take ta yi aiki tare da majalisun dokokin ƙasashen Afrika domin bayar da gudunmawa wajen aiwatar da hakikanin demokuraɗiyya da kuma ingantaccen tsarin demokuraɗiyya mafi dacewa da ƙasashensu, don ci gaba da inganta zaman rayuwar al’ummun dukkan ƙasashen, da bunkasa tsarin demokuraɗiyyar da zai kyautata hulɗar ƙasa da ƙasa.

Fassarawa: Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *