Sin da Equatorial Guinea sun rattaɓa hannu kan musayar bayanai don taimakawa aikin gona a Equatorial Guinea

Daga CMG HAUSA

A ranar 20 ga wata, a ma’aikatar harkokin waje da hadin gwiwar ƙasar Equatorial Guinea, jakadar ƙasar Sin dake ƙasar Equatorial Guinea Qi Mei da ministan harkokin wajen Equatorial Guinea Simeon Oyono Angue, suka rattaba hannu kan musayar bayanai a madadin gwamnatocin ƙasashen biyu, don taimakawa fasahar aikin gona a ƙasar.

Uwar gida Qi Mei ta bayyana cewa, ƙasar Sin tana fatan tallafawa ƙasar Equatorial Guinea, don raya aikin gona na zamani bisa ƙarfin kanta, da inganta ƙarfinta na tabbatar da samar da abinci.

A nasa jawabin minista Simeon Oyono Angue ya bayyana cewa, taimakon da ƙasar Sin ta samarwa ƙasarsa ya haifar da sakamako mai gamsarwa, wanda ya ba da muhimmiyar gudummawa ga ƙoƙarin da ƙasar Equatorial Guinea ke yi na kara samar da amfanin gona, da wadatar abinci.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *