Sin da Indiya sun amince da ƙarfafa tuntuɓar juna domin inganta hulɗarsu

Daga CMG HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi dake ziyara a ƙasar India, tare da takwaransa na ƙasar Subrahmanyam Jaishankar, sun amince su ƙarfafa tuntubar juna a tsakanin ƙasashensu, domin ƙara raya dangantakar dake tsakaninsu.

Yayin tattaunawar da ministocin biyu suka yi a New Delhi, babban birnin India, Wang Yi ya ce ƙasashen Sin da India da suka kasance maƙwabtan juna dake da jimilar al’umma biliyan 2.8, na da muhimmin ƙarfi na tabbatar da daidaito tsakanin ƙasashen duniya da dunƙulewar tattalin arzikin duniya da kasancewar mutane masu mabambantan al’adu tare da taka muhimmiyar rawa ga kyautata hulɗar ƙasa da ƙasa.

Wang Yi ya ƙara da cewa, yayin da duniya ke shiga wani yanayi na ƙalubale da sauye-sauye, ya kamata ƙasashen biyu su ƙarfafa tuntubar juna a tsakaninsu da hada gwiwa kan matsayarsu ta kare halaltattun muradunsu da muradun bai daya na ƙasashe masu tasowa tare da bayar da gudunmuwa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankinsu da ma duniya baki ɗaya.

A nasa ɓangaren, Subrahmanyam Jaishankar ya ce, India na ɗaukar dangantakarta da Sin da muhimmanci, kuma babu abun da ya sauya daga wannan matsaya. Ya ce a shirye ƙasarsa take ta ƙarfafa tuntuɓar ƙasar Sin da kara aminci da juna domin farfaɗo da dangantakarsu daga halin da take ciki nan ba da daɗewa ba, da zummar ba da dama ga ƙulla haɗin gwiwa mai ƙwari.

Yayin taron, ɓangarorin biyu sun amince cewa, farfaɗo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kan yankunan iyakokinsu, muradinsu ne na bai ɗaya, da ya kamata su kula da shi ta hanyar gujewa fito na fito da ɗaukar managartan matakan kaucewa rashin fahimta da yanke bahagun hunkunci.

Fassarawa: Fa’iza Mustaopha