Sin da Nijeriya sun sa hannu kan takardar kafa tsarin haɗin gwiwa tsakanin asibitocinsu

Daga CMG HAUSA

Jakadan ƙasar Sin dake tarayyar Najeriya Cui Jainchun ya gana da ministan kiwon lafiya na Najeriya Osagie Ehanire, inda suka sa hannu kan takardar kafa tsarin haɗin gwiwa tsakanin asibitoci na hukumar lafiya ta ƙasar Sin da ma’aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya.

Sun kuma yi musanyar ra’ayi kan yadda sassan biyu za su kara ƙarfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a ɓangaren kiwon lafiya.

Yayin ganawar da suka yi a Abuja a ranar 19 ga wata, jakada Cui ya bayyana cewa, asibitin al’umma ta jami’ar Peking da asibiti jami’ar Abuja, za su hada gwiwa domin tabbatar da matsayar da aka cimma yayin taron ƙoli na musamman na hadin kan Sin da Afirka domin kandagarkin cutar COVID-19, tare da ƙara ƙarfafa cuɗanya da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a bangaren kiwon lafiya.

Ya ce ƙasar Sin tana son hada hannu da Najeriya domin hanzarta aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin taron tattauna haɗin gwiwar Sin da Afirka.

A nasa ɓangaren, minista Osagie Ehanire ya ce, ya yi farin ciki matuƙa da ganin an sanya aikin kiwon lafiya a gaba da komai yayin da sassan biyu wato Sin da Afirka suke gudanar da haɗin gwiwar a tsakaninsu, yana mai cewa, Najeriya na fatan koyon fasahohin da daga matsayin hadin gwiwarsu, tare kuma da amfanawa al’ummomin ƙasashen biyu.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa