Sin na adawa da ra’ayin Ministan Harkokin Wajen Lithuania game da ƙasar Sin

Daga CRI HAUSA

Rahotanni na cewa, yayin da ministan harkokin wajen ƙasar Lithuania ke ziyara a ƙasar Australia, ya yi kira ga dukkan duniya da su yi adawa da ayyukan keta haƙƙin ɗan Adam da Sin da Rasha suke aikatawa.

Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, ya kamata ƙasar Lithuania ta rungumi gaskiya, ta gyara kuskurenta, ta komawa manufar “ƙasar Sin ɗaya tak a duniya”, kuma ta dakatar da matakai marasa dacewa, da haɗa kan sauran ƙasashe, wajen adawa da ƙasar Sin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *