Sin na fatan Amurka za ta nuna wa duniya sahihancinta

Daga CMG HAUSA

Kalaman da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya yi, yayin tattaunawarsa da takwaransa na ƙasar Amurka Joe Biden ta kafar bidiyo da daren jiya Jumma’a, da ya jaddada cewa, ba raya dangantakar Sin da Amurka bisa hanya madaidaiciya ya kamata ƙasashen biyu su yi ba, akwai bukatar su sauke nauyin dake wuyansu, don kokarin taimakawa ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, sun bayyana hikima gami da sanin ya kamata irin na shugaba Xi.

Ganawar ta kasance ta biyu da shugabannin Sin da Amurka suka yi ta kafar intanet, tun bayan da suka yi shawarwari karo na farko ta kafar bidiyo a watan Nuwambar bara, inda aka samu wasu sabbi da manyan sauye-sauye a duniya bayan watanni huɗu.

A wajen ganawar, Biden ya jaddada cewa, ƙasarsa ba ta neman yin “sabon yakin cacar baka” da ƙasar Sin, ba ta neman sauya tsarin kasar Sin, ba ta kuma neman kyamar ƙasar Sin ta hanyar inganta dangantakar kawance, kuma ba ta goyon-bayan masu kokarin balle Taiwan daga ƙasar Sin, kana, ba ta da niyyar tada rikici da ƙasar Sin.

Shugaba Xi ya ce yana maida hankali sosai kan waɗannan bayanai na Biden, inda kuma a cewarsa, dalilin da ya sa dangantakar Sin da Amurka take cikin wani mawuyacin hali yanzu shi ne, akwai wasu mutanen Amurka da ba su aiwatar da matsayar da shugabannin biyu suka cimma ba, kana, ba su ɗauki matakan zahiri don aiwatar da ra’ayin Biden ba. Amurka ba ta fahimci ainihin manufofin ƙasar Sin ba.

Sa’annan a nasa ɓangaren, shugaba Xi Jinping ya sake ambato batun “nauyin ƙasa da ƙasa” a wannan karo, inda kuma ya sake nanata matsayin gwamnatin ƙasar kan daidaita rikicin Ukraine.

Xi ya kuma ce, a matsayin shugabannin manyan ƙasashe, ya dace su yi la’akari da yadda za su lalubo bakin zaren daidaita matsalolin duniya, da kuma kara la’akari da zaman lafiya da kwanciyar hankali, gami da zaman rayuwar biliyoyin al’ummar duk duniya. Xi ya ce, al’umma za su dandana kuɗarsu idan aka ci gaba da aiwatar da matakan takunkumi daga dukkan fannoni kuma ba tare da wani bambanci ba. Xi ya ƙara da cewa, abun da ya kamata a ba fifiko wajen daidaita rikicin Ukraine shi ne, ci gaba da yin shawarwari, da hana jikkatar fararen-hula da ɓarkewar rikicin jin kai, da kuma tsagaita buɗe wuta tun da wuri.

A wajen ganawar, Biden ya ce yana fatan kara tuntubar ƙasar Sin, don hana ta’azzarar rikicin Ukraine. Kyan alƙawarin cikawa. Amma a lokacin da Amurka take ci gaba da neman hadin-kai da ƙasar Sin, sai kuma ta hada shafawa ƙasar Sin din baƙin fenti gami da yi mata barazana da sanya takunkumi, to wannan kuma abu ne da ba shi da mafita.

Fassarawa: Murtala Zhang