Sin na taka rawar gani a burinta na kaiwa ga ƙololuwar fitar da sinadarin Carbon zuwa nan da shekarar 2030

Daga SAMINU HASSAN

Yayin da duniya ke fuskantar manyan ƙalubalolin dake barazana ga rayuwa, da kiwon lafiyar bil adama, ɗaya daga manyan matsalolin da ake fatan shawo kan su shi ne sauyin yanayi.

A bana, ƙasashe da dama sun fuskanci tsananin zafi dake barazana ga rayuwar al’ummun su, wanda masana da dama ke alakantawa da ƙaruwar dumamar yanayi.

Masharhanta da yawa na ganin manyan ƙasashen duniya sun yi ƙasa a gwiwa, wajen sauke nauyin dake wuyan su, game da sauya akala daga manfani da nau’o’in makamashi masu dumama yanayi, zuwa sabbin makamashi masu tsafta.

Sai dai a gefe guda, ƙasar Sin ta yi nisa wajen aiwatar da manufofinta na daƙile dumamar yanayi, inda a baya bayan nan mahukuntan ƙasar ke cewa, nan da shekarar 2030, ƙasar za ta kai ƙololuwar fitar da sinadarin carbon mai dumama yanayi, daga nan kuma adadinsa ya fara raguwa, zuwa yanayin da zai kai ga kawo ƙarshen tasirinsa baki ɗaya.

Ko shakka babu wannan labari ne mai faranta rai, domin kuwa a matsayin ta na ƙasa mai ci gaban masana’antu, cimma wannan buri zai ba da gagarumar gudummawa, a fannin rage dumamar yanayi a duniya baki ɗaya.

Abun fatan dai shi ne, sauran manyan ƙasashen duniya, musamman masu ci gaban masana’antu, za su zage damtse wajen sauke nauyin dake wuyan su, a fannin rage tashoshin sarrafa makamashi daga abubuwa masu haifar da dumamar yanayi, su kuma karkata ga amfani da nau’o’in makamashin da ake iya sabuntawa, domin kuwa daukacin bil adama na rayuwa ne cikin wannan duniya kwaya ɗaya, don haka kare muhallin duniya, nauyi ne kan dukkanin al’ummun duniya baki ɗaya.