Daga CMG HAUSA
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya bayyanawa taron manema labaru da aka saba shiryawa Alhamis din nan cewa, duk wasu ƙarairayi da jita-jita masu nasaba da jihar Xinjiang ta ƙasar Sin, gaskiya za ta yi halin ta, kuma yunƙurin da wasu ƙasashe ke yi na neman bata sunan ƙasar, ta hanyar amfani da wasu batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang ba za su taba yin nasara ba.
An bayar da rahoton cewa, kimanin ƙungiyoyi masu zaman kansu na gida da wajen ƙasar Sin dubu 1 ne, suka aike da wasiƙar haɗin gwiwa ga babbar jami’ar kare hakkin dan-Adam ta MDD Michelle Bachelet, domin nuna adawarsu game da rahoton da ofishin ya fitar kan jihar Xinjiang.
Zhao Lijian ya jaddada cewa, ƙasar Sin tana kira ga hukumar OHCHR, da ta mutunta babban damuwar jama’ar ƙasar Sin da dukkan mutane masu sanin ya kamata a duniya, da tsayawa kan ɓangaren tarihi, da kin wallafa rahotannin da suka shafi jihar Xinjiang ta ƙasar Sin bisa bayanan karya da kuma zarge-zarge.
Fassarawar Ibrahim