Sin ta ƙalubalanci wasu kamfanonin Amurka

Daga CRI HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce Sin ta ƙalubalanci kamfanonin Raytheon da Lockheed Martin na Amurka, saboda hannu da suke da shi a sayarwa yankin Taiwan na Sin makamai, matakin dake da illa ta fuskar ‘yancin mulkin kai da tsaron ƙasar Sin.

Wang Wenbin ya ce Sin ta sake jaddada kira ga gwamnatin Amurka, da sauran sassa masu ruwa da tsaki da su martaba manufar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, da yarjejeniyoyin da sassan biyu suka sanyawa hannu, kana ta dakatar da sayarwa yankin Taiwan makamai, da ma ƙulla duk wata cuɗanyar da ta shafi ayyukan soji ga yankin.

Jami’in ya ce Sin za ta ci gaba da ɗaukar dukkanin matakan da suka wajaba gwargwadon sauyawar yanayi, za ta kuma kare moriyar mulkin kai da tsaron ta yadda ya kamata.

Fassarawa: Saminu