Sin ta ɗau matsaya mafi dacewa game da batun Ukraine

Daga CMG HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya bayyana a jiya Asabar cewa, ƙasar Sin tana kan matsaya ta adalci game da batun Ukraine, kuma lokaci ne zai tabbatar cewa, ta dauki matsaya mafi dacewa a tarihi.

Wang, ya yi wannan tsokaci ne a yayin da yake jawabi ga ‘yan jaridu game da musayar kalaman da aka yi tsakanin shugabannin ƙasashen Sin da Amurka kan batun Ukraine, inda suka tattauna ta kafar bidiyo a ranar 18 ga watan Maris.

Wang Yi ya bayyana cewa, ƙasar Sin ta bayyana a fili ƙarara game da matsayarta kan batun Ukraine. Abu mafi muhimmanci shi ne, a ko da yaushe ƙasar Sin burinta shi ne tabbatar kiyaye zaman lafiyar duniya.

Ministan harkokin wajen ƙasar Sin ya nuna cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da tsayawa kan manufarta na tabbatar da adalci bisa tsari na adalci ga kowane ɓangare kan wannan batu. Wang ya ƙara da cewa, ƙasar Sin ba za ta taba yin ƙasa a gwiwa kan matsayarta sakamakon matsin lamba daga kowane ɓangare ba, kuma tana adawa da dukkan wasu zarge-zarge marasa tushe da ake yi mata.

Ya ci gaba da cewa, babban abin da ake baiwa fifiko shi ne, tilas ne dukkan ɓangarori masu ruwa da tsaki su yi kokarin ingiza matakan tattaunawar sulhu, da kuma gaggauta cimma daidaito a tsakanin ɓangarorin, da kawar da kiyaye ba tare da bata lokaci ba, da dena kashe fararen hula, kana a kawar da duk wani shinge da zai kawo cikas ga ayyukan jin kan bil Adama.

Hanya mafi dacewa ta kawo ƙarshen rikicin ya dogara ne kan kaucewa amfani da halayyar yakin cacar baka, da kaucewa amfani da hanyoyi na yin fito-na-fito, kuma a gina ingantaccen tsarin adalci na tabbatar da tsaron shiyya-shiyya, domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a nahiyar Turai, in ji minista Wang.

Fassarawa: Ahmad