Sin ta ciri tuta wajen tallafa wa masu buƙata ta musamman

Daga SAMINU ALHASSAN

Ga duk mai bibiyar manufofin ƙasar Sin, waɗanda suka jibanci ƙara inganta rayuwar alumma, ba zai gaza lura da yadda mahukuntan ƙasar ke bullo da shirye-shirye daki-daki ba, na kyautata rayuwar sassan alummun ta masu buƙatu na musamman, da suka haɗa da masu nakasar sassan jiki, ko rashin lafiya, ko tsufa.

Akwai tarin manufofi da mahukuntan ƙasar ke tsarawa, domin ganin dukkanin sassan masu buƙatar musamman a ƙasar sun more rayuwa mai inganci cike da walwala.

Ga misali, ƙasar Sin ta tsara shirye shirye na musamman, domin kula da lafiyar tsofaffi, musamman wajen samar musu da hidimomin rayuwar yau da kullum, da matsugunai masu inganci, da kula da lafiya, da inganta unguwannin da suke zaune, da samar da inshorar lafiya da dai sauran su.

A ɓangaren wasanni, a ranar Alhamis ɗin nan, majalissar gudanarwar ƙasar Sin ta fitar da takardar bayani mai ƙunshe da fashin baki, game da irin ci gaban da ƙasar ta samu, a ɓangaren raya shaanin wasanni, tsakanin rukunin mutane masu buƙata ta musamman.

Takardar na zuwa a gabar da ake daf da bude gasar Olympics ta shekarar 2022, ajin masu buƙatar musamman ko Paralympic, wadda birnin Beijing ke karɓar baƙunci.

Ko shakka babu, tun bayan kafuwar jamhuriyar jamaar ƙasar Sin, an riƙa samun manyan nasarori a fannonin kyautata rayuwar masu buƙata ta musamman, inda gwamnatin ƙasar Sin ke kara bunƙasa harkokin wasannin wannan rukuni na alummar Sinawa, bisa halin da ƙasar ke ciki da ma buƙatu na zamantar da rayuwa.

Irin waɗannan manufofi da tsare-tsare, da gwamnatin Sin ke aiwatarwa, nasarori ne manya da suka zamo zakaran gwajin dafi a tarihin duniya, wato batun tafiya tare da dukkanin sassa, da rukunonin alummar ƙasa ba tare da nuna wariya ba, kamar dai yadda sau da dama, a kan ji shugaban ƙasar Sin Xi Jinping na nanata cewa, burin gwamnatin ƙasar Sin shi ne inganta rayuwar alummar ta, ba tare da barin kowa a baya ba!

Fasaarawa: Saminu Alhassan