Daga CRI HAUSA
A Alhamis ɗin nan ne ƙasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken “wasannin masu buƙatar musamman”, wadda ke ƙunshe da fashin baki game da irin ci gaban da ƙasar ta samu, a ɓangaren raya wasanni tsakanin rukumin mutane masu buƙata ta musamman.
Majalissar gudanarwar ƙasar Sin ce ta fitar da takardar bayanin, kwana guda kafin buɗe gasar Olympics ta 2022, ajin masu buƙatar musamman ko Paralympic, wadda birnin Beijing ke karɓar baƙunci.
Takardar bayanin ta ce, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin a shekarar 1949, ake ta samun ci gaba a fannonin kyautata rayuwar masu bukata ta musamman, kuma ƙasar Sin ke ƙara bunƙasa wasannin wannan rukuni na al’ummarta, bisa halayyar musamman ta ƙasar, da kuma martaba tafiya da zamani.
Kazalika takardar bayanin ta taɓo irin nasarori da aka cimma a tarihi, a ɓangaren raya wasannin masu buƙatar musamman tun bayan taro na 18, na JKS da ya gudana a shekarar 2012.
Fassarawa: Saminu Alhassan