Sin ta kyautata tsarinta na zuba jari da tattara kuɗi tsakanin ta da sauran sassan ƙasa ƙa ƙasa

Daga CMG HAUSA

Bisa rahoton hada-hadar kuɗaɗe da aka samu, da waɗanda aka kashe tsakanin ƙasa da ƙasa na farkon rabin shekarar 2022 na ƙasar Sin, wanda hukumar kula da musayar kuɗaɗe ta ƙasar Sin ta fitar a kwanakin baya, Sin ta kara zurfafa buɗe kofa ga ƙasashen waje, a ƙarin yankuna da fannoni daban daban, wanda hakan ya sa ƙaimi ga kyautata tsarin Sin na zuba jari da tattara kuɗi a tsakanin ƙasa da kasa.

Rahoton ya bayyana cewa, tare da kyautata yanayin cininki a cikin ƙasar Sin, an samu kyakkyawar kasuwar kashe kuɗi a ƙasar, don haka kamfanonin ƙasa da ƙasa suka fi son zuba jari ko kafa kamfanoni a ƙasar Sin.

Rahoton ya nuna cewa, ya zuwa farkon rabin shekarar 2022, yawan jarin da kamfanonin ƙasashen waje suka zuba kai tsaye a ƙasar Sin ya kai dalar Amurka triliyan 3.6, adadin da ya ƙaru da kashi 73 cikin dari bisa na ƙarshen shekarar 2012.

Kana bunƙasuwar ƙarfin kamfanonin Sin, ta sa su fi buƙatar fita waje, hakan ya sa yawan jarin da kamfanonin Sin suka zuba ga ƙasashen waje kai tsaye, ya ƙaru daga dalar Amurka biliyan 500 a ƙarshen shekarar 2012, zuwa dalar Amurka triliyan 2.6 a farkon shekarar 2022.

Mai fassara: Zainab

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *