Sin ta samar da yanayi maras gurɓata muhalli a gasar cin kofin duniya na Qatar

Daga CMG HAUSA

A jiya Lahadi 20 ga watan nan ne aka buɗe gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya a Qatar.

Duk da cewa tawagar ƙwallon ƙafar Sin ba za ta buga gasar ba, ana iya ganin alamomin ƙasar Sin a gasar ta bana, musamman ma fannin manyan ababen more rayuwa da aka gina, ciki har da filin wasa, da aikin samar da ruwa, da na samar da lantarki, waɗanda ƙasar Sin ta taimakawa wajen samar da su.

Babban filin wasa na Lusail mai ɗaukar ’yan kallo 80,000, shi ne mafi girma da za a yi amfani da shi a gasar ta bana, kuma a nan ne za a gudanar da wasanni 10, ciki har da wasan ƙarshe.

Kamfanin CRC na ƙasar Sin ne ya gina filin na Lusail, kuma shi ne filin wasan ƙwallo na gasar cin kofin duniya na farko da wani kamfannin ƙasar Sin ya aiwatar da gininsa tun daga tushe, inda kamfanin ya yi nasarar kawar da babakeren ƙasashe Turai da Amurka a wannan fanni.

Babban sakataren tsare-tsare na gasar ta bana Hassan Al Thawadi ya ce, Qatar ta yi na’am da ingancin ginin filin wasan na Lusail.

Filin na da nau’o’in rumfunan ’yan kallo daban daban, kuma kammala ginin sa cikin nasara, shaida ce dake tabbatar da ƙwarewar aiki ta kamfanonin ƙasar Sin.

Mai Fassarawa: Saminu Alhassan