Sin ta samu ci gaba a ginin tashar sadarwa ta 5G

Daga CMG HAUSA

Ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta ƙasar Sin, ta ce adadin tashoshin samar da tsarin sadarwa na 5G dake ƙasar Sin na ƙaruwa, yayin da kasar ke ƙoƙarin inganta ginin tsarin sadarwar a shekarun baya bayan nan.

Alƙaluma daga ma’aikatar sun nuna cewa, zuwa ƙarshen watan Agusta, ƙasar Sin na da tashoshin 5G sama da miliyan 2.1, wanda ya ɗauki kaso 19.8 na tashoshin samar da 5G din ga na’urorin tafi da gidanka, adadin da ya ƙaru da kaso 5.5 daga ƙarshen shekarar 2021.

Haka kuma, cikin watanni 8 na farkon bana, an gina ƙarin tashoshin 5G 677,000 a ƙasar.

Har ila yau, ma’aikatar ta ce adadin masu amfani da 5G a na’urorin tafi da gidanka a ƙasar Sin, ya kai miliyan 475 a ƙarshen watan Yuli.

Rahoton hukumar ƙididdiga ta ƙasar Sin ya ruwaito cewa, ƙasar ta gina tsarin sadarwar 5G mafi girma a duniya.

Kuma zuwa ƙarshen shekarar 2021, adadin tashoshin 5G a ƙasar ya ɗauki sama da kaso 60 na duniya baki ɗaya.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha