Sin ta yu kira da a yii bayani game da batun tsaro da ya shafi ƙwayoyin halittu masu haɗari a Ukraine

Daga CMG HAUSA

Zaunannen wakilin Ƙasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki game da batun ƙwayoyin halittu masu hadari a Ukraine, da su yi bayani game da daftarorin da aka gano a baya-bayan nan, domin kawar da shakku daga zukatan al’ummun duniya.

Ya ce ƙasar Sin ta taɓa fama da tasirin makamai masu guba da ƙwayoyin halittu masu hadari. Kuma ta yi ammana cewa, ya kamata duk wani bayani game da ayyukan soji da suka shafi ƙwayoyin halittu masu hadari, ya ja hankalin al’ummun duniya domin kare aukuwar haɗari mai muni.

Zhang Jun, ya shaidawa Kwamitin Sulhu na MDD cewa, ya kamata dukkan masu ruwa da tsaki su ɗauki matakin da ya dace. Ya ce Rasha ta ƙara bayyana wasu daftarori da ta gano a baya-bayan nan, don haka, kamata ya yi waɗanda abun ya shafa, su amsa tambayoyin da ake da su, tare da yin bayani akan kari, domin kawar da shakku.

Ya ce matsayar ƙasar Sin kan makaman kare dangi a bayyane take, kuma ba ta sauya ba. A cewarsa, Sin na goyon bayan haramtawa da lalata dukkan makaman ƙare dangi, ciki har da masu guba da ƙwayoyin halittu masu hadari.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha