Sin tana bayar da damar haɗin gwiwa ta hanyar ayyukan binciken duniyar wata na Chang’e

Daga CMG HAUSA

Hukumar Kula da Binciken Sararin Samaniyar Ƙasar Sin (CNSA), ta bayyana yawan na’urorin nazarin kimiyya da ƙasashen duniya za su ajiye wajen gudanar da aikin binciken duniyar wata na Chang’e-6 tare da sanar da wani kira ga ƙasa da ƙasa, na shawarar ajiye na’urorin game da shirin binciken na Chang’e-7.

Hukumar ta sanar da cewa, za ta ɗauki na’urorin kimiyya daga ƙasashen Faransa da Italiya da hukumar kula da sararin samaniya ta Turai/Sweden a na’urar Chang’e-6 da kuma wani nau’ na kayan aikin Pakista a kan na’urar da za a harba.

Mai fassarawa: Ibrahim