Sin tana cin zaluncin Musulmai ƙarya ce!

Daga AMINA XU

Abokaina a duniya a zanen MINA sun yi min sako cewa, game da haƙƙin Bil Adama, an ji an ce Sin ta cin zaluncin musulmai, ko za ki iya zanen hoto game da zaman rayuwarsu? To, a wannan karo na zane wani Cartoon dangane da wata azumi. Ran 2 ga wannan wata an shiga watan azumi, musulmai a wurare daban-daban a ƙasar Sin sun fara azumi, Cartoon da nake zana na dangane da haƙiƙanin halin da musulmai dake yankin Xinjiang mai Uygur suke ciki, ga yadda suke yin sallah a watan azumi. Kowa ya sani yankin Xinjiang na da musulmai masu ɗimbin yawa, bisa ƙididdigar da yankin ya gabatar, a shekarar 2000 yawan ƙabilar Uygur ya kai miliyan 8.34, a shekarar 2020 kuma ya karu zuwa miliyan 11.62.

Idan aka yi musu zalunci, to yaya yawan Uygur ya samu ƙaruwa cikin sauri? Idan ba a manta ba, Indiyawan daji yawansu sun ragu daga miliyan 5 zuwa dubu 250 saboda kisan gillar da Amurka ta yi musu, wannan shi ne cin zalunci da kisan ƙare-dangi. Abokai, idan ku bude idanunku ku gani hakikanin hali da Sin take ciki, za su fahimci cewa, Musulmai a nan kasar Sin suna da ‘yancin aiwatar da harkokin addini cikin ‘yanci, duk wata magana wai Sin ta cin zaluncinsu, ba shakka karya ce!

Mai zane: Amina Xu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *